Ka da ka shekara 10 da mata daya —Sheikh Daurawa

 Ka da ka shekara 10 da mata daya —Sheikh Daurawa


Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shawarci maza cewa ka da su kuskura su shekara 10 da mace daya matukar suna da burin kara aure. Jaridar Aminiya ta ruwaito
.

Sheikh Daurawa, ya bayyana haka ne a zantawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano haka ne, inda ya ce idan namiji ya kai wannan shekarun da mace daya, lokaci ya kure masa.

“Kada ka wuce shekara 10 idan za ka kara aure ba ka kara ba. Idan ka wuce shekara 10 akalla kana da ‘ya ‘yar shekara takwas ko tara.

“Da zarar ’yarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da ’yarka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba.

“Saboda haka matarka ta samu abokiyar rigima. Akwai wadda za ta iya tura ’yarta ta samu amarya su rika rigima ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi karfinta.

“…Saboda haka wanda zai yi aure ya shirya da wuri, kuma kada duk dadin miyar mace ka ce ba za ka kara aure ba,” in ji Shehun malamin.

Karin aure ko yi wa uwar gida kishiya na tayar da kura a lokuta da dama, lamarin da ke haifar da mummunan kishi a tsakanin kishiyoyin.

A wasu lokuta ma ana rasa zaman lafiya a gidan, wanda hakan yakan kai ga yin saki don samun kwanciyar hankali.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN