An kashe mutane 13, an sace 73 a harin da 'yan bindiga suka kai a Sokoto


‘Yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da wasu 73 da suka hada da mata da kananan yara a gabashin jihar Sokoto. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

An kai hare-haren ne a al’ummomi daban-daban a fadin kananan hukumomi uku da suka hada da Sabon Birni.

An tattaro cewa an kai hare-hare kusan a lokaci guda a ranar Litinin, 26 ga watan Disamba.

Da yake zantawa da Daily trust, wani mai rike da sarautar gargajiya a Sabon Birni, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kai wa wasu kauyuka uku hari a karamar hukumarsa sannan aka kashe mutum 11.

Al’ummomin su ne Gatawa da Dangari inda aka kashe mutum shida, biyu a Gatawa, uku kuma a Kurawa.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban kungiyar ‘yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad, da dan Majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a Majalisar dokokin jihar, Aminu Almustapha Boza, sun ce an kashe marigayin ne a gonar da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.

Boza ya ce maharan sun yi garkuwa da mutane da dama.

Shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, wanda ya yi tir da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummomin, ya ce an kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 23 a yankin Shinaka da Kagara a ranar Litinin da ta gabata.

Hakazalika, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gada ta gabas a majalisar dokokin jihar, Kabiru Dauda, ​​ya shaida wa manema labarai cewa, wasu ‘yan bindiga sun sace sama da mutane 50 da suka hada da mata da kananan yara a yankin ranar Litinin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN