Dan Hisbah ya aikata mugun laifi, Kotu ta yanke masa hukuncin kisa a jihar arewa mai tasirin addini


Dayyabu Muhammad, wani tsohon dakaren Hisbah ya gamu da fushin alkali yayin da aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a wata kotun jihar Kano mai lamba 9. Legit.ng ta wallafa.

Mai shari’a Amina Adamu ce ta yanke hukuncin bayan da ta kama jami’in na Hisbah da laifin kashe bazawarsa mai suna Hauwa.

Laifin kisan bazawarar tasa ya saba doka, don haka aka yanke masa hukunci daidai da kunfin Panel Code sashe na 221.

Alakar Dayyabu da Hauwa da hukumar Hisbah

Rahoton da muka samo daga Aminiya ya bayyana cewa, Dayyabu ya kasance almajiri a gidansu Hauwa, kuma jami’i ne na Hisbah wanda ya nuna sha’awarsa ta auren Hauwa, daga nan suka kulla soyayya.

Yayin da Dayyabu ya zo da maganar aure, iyayen Hauwa sun ce ba za su bashi ita ba saboda suna ganin akwai tangarda a tarbiyyarsa, wannan yasa Hauwa daga baya ta sauya ra’ayi a kansa, tace bata yi.

Yadda Dayyabu ya kashe Hauwa

Wannan lamari dai ya fusata Dayyabu, inda ya zo har gida a shekarar 2011 har daki ya nemi ganin Hauwa.

An ruwaito cewa, a nan ya dauko wuka ya caccaka mata a jikinta, kuma wannan dai shi ne sanadin mutuwarta.

Bayan samun gamsassun hujjoji, mai shair’a Amina Adamu ta ce ta gamsu da komai da aka gabatar na hujja, don haka ta yanke masa hukunci.

Yanzu dai an yanke masa hukunci ta hanyar rataya, amma ba a san ko hakan zai tabbata ba, domin ana yanke hukunci a samu sabanin hakan.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN