Taron gangamin APC a Minna: Ko da gaske an garzaya da Tinibu daga fage saboda matsalar lafiya? Kakakin yakin neman zaben ya mayar da martani


Jam'iyyar APC ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa an garzaya da dan takararta na shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu daga dandalin taron gangamin da ya gudanar a garin Minna na jihar Neja saboda rashin lafiya. Legit.ng ta wallafa.

Bayo Onanuga, daraktan watsa labarai da wayar da kan jama'a, Majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba a shafin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.

Taron gangamin jam’iyyar APC a Minna: Dalilin da ya sa Tinubu ya fice da wuri

Onanuga ya ce Tinubu ya bar taron ne da sanyin safiyar Laraba, 14 ga watan Disamba, domin halartar sauran shirye-shiryen ranar.

A cewar kakakin kamfen din, jama’ar da suka fito domin tarbar Tinubu a wurin taron sun yi yawa har tsohon gwamnan jihar Legas ya yi musu jawabi a takaice.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Taron ya yi yawa har Tinubu ya yi magana a takaice domin ya yaba wa magoya bayansa tare da tantance ‘yan takarar jam’iyyar da ke neman mukaman zabe.

“Sabanin jita-jitar cewa an garzaya da shi ne saboda rashin lafiya, Tinubu ya yanke shawarar halartar sauran shirye-shiryen ranar.

"Ya yabawa magoya bayan jam'iyyar da suka fito gadan-gadan domin shaida tutar yakin neman zaben shugaban kasa."

Inda Tinubu ya je bayan ya bar taron da wuri, Onanuga ya bayyana

A cewar sanarwar, Tinubu ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a Minna bayan ya tashi daga taron.

Legit.ng ta tattaro cewa Mawallafin Jaridar Blueprint kuma Shugaban, Strategic Communications na Asiwaju Bola Tinubu Presidential Campaign Council (PCC), Alhaji Mohammed Idris Malagi ne ya ba da gudummawar ofishin.

Tinubu ya kuma ziyarci Sarkin Minna, daga bisani kuma ya samu liyafar cin abinci da Gwamnan Neja, Abubakar Bello ya shirya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN