An kama matar aure da ta taimaka wa mijinta wajen yin garkuwa da mutane


Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta kama wata ‘yar shekara 36 mai ‘ya’ya takwas, Bilkisu, bisa zarginta da taimakawa mijinta, Nafiu Yusuf, wajen yin garkuwa da mutane.

Wanda ake zargin da mijinta, wadanda jami’an rundunar ‘yan sandan suka kama, na daga cikin mutane 27 da Kwamishinan ‘yan sanda, S.K Akande, ya gabatar a ranar Laraba, 30 ga Nuwamba.

A cewar rundunar ‘yan sandan, an kama matar ne biyo bayan kama mijinta wanda a karshe ya jagoranci ‘yan sandan zuwa gidansa domin bincike.  An gano cewa tana taimaka wa mijinta wajen boye bindigar AK-47 da yake amfani da shi wajen aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Da aka tambaye ta, Bilkisu ta musanta zargin, amma ta yi ikirarin cewa lokacin da ta ga makamin a karkashin gadonsu, sai ta yanke shawarar daukar makamin ta ajiye a wani wuri saboda tsoron ‘ya’yanta.  A cewarta, ba ta taba ganin irin wannan makami ba, ballantana ta taba, kuma ta ga bayan mijinta ya tafi gona. 

Ta yi ikirarin cewa ta boye makamin ne tsawon kwanaki uku ba tare da sanin cewa an kama mijin nata ba.  Ta kara da cewa kuskuren da ta tafka shine rashin kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

A nasa bangaren, Nafiu, ya ce bai taba aikata laifi da ita ba, kuma an ba shi bindigar ne domin a kai shi ga wani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN