Ko da yake ana sa ran cewa ‘yan takarar shugaban kasa a zabukan Najeriya sun lashe jihohin da gwamnonin ke cikin jam’iyyunsu, akwai yiwuwar a samu wasu ketare a 2023. Legit.ng ta ruwaito.
Saboda akalla abubuwa biyu, mai yiwuwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kasa yin nasara a wasu jihohin da gwamnonin ke zaune a jam’iyya mai mulki.
Jihohin sun hada da:
Jihohin Cross River Ebonyi Imo Kwara da Ogun.
Idan har ba a magance rikicin gabanin kada kuri’a ba, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na iya yin amfani da wannan damar wajen ganin PDP ta yi wa Tinubu illa a yankin arewa ta tsakiya.
Jihohin Imo da Ebonyi
Shiyyar kudu maso gabas ba masoyan jam'iyyar APC mai mulki bane. Tun a shekarar 1999, yankin da 'yan kabilar Igbo ke da rinjaye suka zabi jam'iyyar PDP.
A 2023, yanzu suna da zabi biyu: PDP ko Labour Party, wanda ke tsayar da dan su Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Don haka, duk da cewa gwamnonin Imo da Ebonyi na APC, da wuya Tinubu ya kayar da Atiku ko Peter Obi a jihohin Kudu maso Gabas biyu a zaben 2023.