Bayan an garkame miji a Kurkuku sakamakon yi wa matarsa dukan tsiya, mata ta yo belinsa duk da zagi da cin mutunci da yake mata


Wata mata ‘yar Najeriya ta yi belin mijinta ‘mai zagi’ daga gidan yari bayan da aka kama shi kuma aka tsare shi da laifin yi mata dukan tsiya.

Wata kungiya, DPA Family Law Clinic, ta bayyana hakan a cikin wani sakon Facebook a ranar Alhamis, 24 ga Nuwamba.

“Mun kama mijin nata, aka tsare kan laifin dukanta da yi, ‘yan uwansa suka ki zuwa domin su amshi belinsa, suka ce sai dai ya mutu a nan, sai matar ta bi bayanmu ta karbi belinsa.

“Matar ta biya kudi 10k ta karbi belin mijinta saboda mutanensa sun ki zuwa, ta ce ko da sun kai mijin kotu to zai yi zaman gidan yari kuma ba za ta iya jurewa ba, ita ce ke biyan duk wasu kudade, harda haya domin baya aiki."

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE