Yara makiyaya sun gurfana a Kotu sakamakon banka wuta da gangan a gonar gyada a jihar Kebbi


Wasu yara makiyaya guda uku sun gurfana a gaban Kotun Majistare a garin Birnin kebbi bayan sun banka wuta a gonar wani manomi da gangan. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Yaran masu suna Riskuwa Mode, Sanda Kiruwa da Manu Kinasa sun gurfana a gaban Mai Sharia Hassan Muhammad Kwaido bisa zargin haddasa barna ta hanyar tayar da gobara da gangan (Mischief by fire) lamari da ya ja wa mai gona hasarar gyada da aka kiyasta kudinsa Naira miliyan daya da dubu dari biyar N1.5m. 

Lamarin ya faru ne a Mashekarin Geza da ke kusa da garin Bunza a karamar hukumar Bunza da ke jihar Kebbi. Sakamakon haka aka gurfanar da su a gaban Kotu ranar 28/10/2022.

Riskuwa Mode ya shaida wa Kotu cewa "Tare da Sanda da Manu muka je gonar, amma ni na sa wuta a gonar sai muka wuce". 

Ya ce " Mun taba sa dabbobi sun yi barna a gonar sai mai gona ya kai kara aka sa mu biya, aka sayar da saniya aka biya shi, sakamakon haka na sa wa gonar wuta" in ji shi. 

Bayan Lauyan yaran Barista Y.A Aminu daga ofishin Lauyoyi na Marshal & Associates ya gabatar da bayai gaban Mai sharià bisa ayoyin doka.

Mai Sharia ya umarci a nemo wadanda za su karbi Sanda da Manu, yayin da ya yi umarni a mayar da Riskuwa gidan Remand har zuwa ranar 6 ga watan Disamba 2022 domin ci gaba da sharia'ar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN