Ma'aikatar Sharia sashen babbar Kotun daukaka kara na sharia'ar Musulunci a jihar Kebbi ta rantsar da sabbin Alkalai na Kotunan shari'ar Musulunci ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba 2022 a garin Birnin kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Mukaddashin Grand Khadi na jihar Kebbi Dr Tukur Sani Argungu tare da babban Jojin jihar Kebbi CJ Muhammad Sulaiman Abursa da sauran Khadi suka jagoranci tsarin rantsarwar na ranar Litinin a cikin babbar Kotun daukaka kara na sharia'ar a Birnin kebbi.
Wadanda aka nada a mukamin Alkalai aka kuma rantsar da su sun hada da:
1. Rufa'i Liman Ambursa
2. Saddi Zaki Ambursa
3. Malami Shehu
4. Bashar Bala
5. Abubakar Sahabi Kawara
6. Ibrahim Abubakar Kaya
7. Umar Ibrahim Mai Ahu
8. Sulaiman Sani Jaja
9. Rilwanu Malami
10. Saddik Hussaini
11. Sirajo Usman Kamba
12. Yusuf Muhammad Wakili
13. Abubakar Muhammad 2
14. Aminu Muhammed Dandare
15. Sa'idu Muhammed Argungu
16. Nura Muhammed Kalgo
17. Aminu Attahiru
18. Rasheed Kabiru
19. Muhammed Shehu
20. Rilwanu Muhammed Lawal
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI