Type Here to Get Search Results !

Yan sandan jihar Kebbi sun kama masu aikata manyan laifuka da makasan wani manomi saboda kishin nassarorin amfanin gona da yake samu


Hukumar yan sanda jihar Kebbi ta yi nassarar kama wadanda ake zargin da aikata wasu manyan laifuka a fadin jihar. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Kwamishinan yansandan jihar CP Ahmed Magaji Kontagora ya sanar da kamen yayin jawabi ga manema labarai a garin Birnin kebbi ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamba a Shelkwatar Yan sanda a Birnin Kebbi.

Magaji ya ce rundunarda ta yi nassarar kama wasu mutane da ake  zargin da kashe wani manomi mai suna Samaila Kamuna daga garin Rijau a jihar Neja ya je kauyen Bature a garin Ngaski domin gabatar da harkar nomanshi, ya sauka a wajen wasu mutane amma suka halaka shi saboda kishin nassarori da yake samu a harkar noma. Magaji ya ce yansanda sun kama wadanda ake zargin kuma suna fuskantar bincike.

Kazalika ya ce yansanda sun kama wani mai suna Ayuba Rege dan garin Tadurga mai shekara 20 da bindiga a Jakar shi na makaranta, kuma yana fuskantar bincike a hannun yan sanda.

Kazalika yan sanda sun kama wani mai suna Ahmed Ibrahim mai shekara 35 a garin Kasuwar gari da ke Dirin daji a karamar hukumar Sakaba bayan ya yi wa wata yarinya yar shekara 14 mai suna Zuwaira Abubakar ciki sakamakon saduwa da ya dinga yi da ita har sau bakwai ba tare da aure ba.

Ya ce yansanda da yan bang da ke sintiri a hanyar Maiyama da Koko sun kama wasu mutane guda biyu da babur, Mustapha Abubakr dan shekara 30 daga Dange shuni a jihar Sokoto da Lawali dan shekara 30 daga garin Tambuwal, bayan tuhumarsu sun tabbatar cewa sun sato babur din ne daga wani gari a karamar hukumar Ngaski. Sakamakon haka an kama wasu mutane da suka hada da Buhari, Sa'adu da Abdullahi bisa zargin laifin karbar kayan sata.

Kwamishinan yansandan jihar ya kuma yi kira ga jama'a su guji daukar doka a hannu, ya yi kira cewa jama'a su dinga kai kokensu ga jami'an tsaro domin bi masu kadin hakkinsu.


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies