Jiragen saman yaki na kasar Poland sun jagoranci jirgin sama dauke da Yan kwallon kafa zuwa kan iyakar kudancin kasar bayan wani makami mai linzami da ya halaka manoma biyu mai nisan kilomita hudu daga kan iyakar Ukraine.
Tawagar da suka hada da Super star, Robert Lewandowski, jiragen yakin F-16 ne suka raka ta daga kasar a kan hanyar zuwa gasar cin kofin Duniya a Qatar.
Jiragen saman yakin na kasar Poland ne suka jagorance su zuwa kudancin kasar Poland bayan wani makami mai linzami da ya halaka manoma biyu mai nisan kilomita hudu daga kan iyakar Ukraine a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba.
Bayan fashewar, sojojin sun rufe kan iyakar Ukraine da Poland saboda fargabar rikicin bakin haure na Rasha.
Tawagar kasar Poland, za ta fara gasar ta da Mexico ranar Talata 22 ga watan Nuwamba.
Poland ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya na baya-bayan nan, kuma bayan da ta yi waje da ita a matakin rukuni a 2018, za ta yi fatan za ta kara gaba da zuwa matakin bugun gaba a karon farko tun 1986.
Rubuta ra ayin ka