Wata mata ‘yar Najeriya ta bayar da rahoton cewa an yi mata fyade a cibiyar karbar masu neman mafaka a Pournara da ke Kokkinotrimithia a kasar Cyprus. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Lamarin da ake zargin ya faru ne bayan tsakar daren ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba, inda ake zargin wasu mutane biyar daga Najeriya, kamar yadda wasu ‘yan sanda suka bayyana.
Ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ake tuhumar mutanen biyar da ake zargi da aikata laifin.
Ba shi ne karon farko da wani mai neman mafaka a cikin cunkoson Pournara ya ba da rahoton an yi masa fyade ba.
‘Yan sanda sun shaida wa Knews a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, cewa ba a gano wadanda ake zargi da aikata laifin ba, inda suka kara da cewa ofishin ‘yan sanda na Kokkinotrimithia da CID Nicosia na gudanar da bincike kan zargin.
An bayyana cewa wani likita ya duba wanda aka yi wa fyade, yayin da aka ce ‘yan sanda suna jiran sakamako domin sanin matakin gudanar da bincikensu.
Rubuta ra ayin ka