Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe yan sanda


Tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a ranar Asabar, yayin wani farmaki da suka kai shingen bincike na yan sanda a garin Agbani da ke karamar hukumar Nkanu ta jihar Enugu. Legit.ng ta wallafa.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yan bindigar sun kai mamaya shingen binciken da misalin karfe 8:00 na safe sannan suka budewa jami’an yan sandan da ke bakin aiki wuta inda suka kashe uku a nan take.

Tashar binciken yan sandan na kusa da hedkwatar rundunar na Agbani.

Vanguard ta kuma rahoto cewa jami’an yan sandan na aikin binciken ababen hawa ne lokacin da makasan suka hange su sannan nan take suka bude masu wuta wanda ya kai ga mutuwar jami’ai uku.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana sunansa da Ifeanyi ya bayyana yadda lamarin ya afku.

Ya ce:

“Jami’an yan sanda sun mayar da hankali wajen karbar kudi daga yan achaba da+ direbobin bas ne lokacin da yan bindigar suka farmake su. Lamarin ya faru ne kamar kyafta ido.

“Da yawanmu mun tsere a lokacin da muka ji karar harbi. Mun dawo kawai sai muka ga gawarwakin yan sanda uku.”

Wani bidiyo da aka dauka bayan faruwar lamarin na ta yawo a shafukan soshiyal midiya.

A cikin bidiyon, an gano gawarwakin jami’ai biyu kwance a kasa a gefen wani babban titin

An jiyo wata murya a kasan bidiyon tana cewa:

“Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe jami’an yan sanda yanzun nan. Daya daga cikinsu ya tsere, amma an kashe uku. Kalli gawarwakinsu a nan.”

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ba don baya amsa kiran waya da sakonnin da ke neman jin ta bakinsa kan harin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN