Wata mata ta sauka daga taksi, ta yi tsalle ta tsunduma cikin tafkin Legas

Wata mata ta sauka daga taksi, ta yi tsalle ta tsunduma cikin tafkin Legas


Wata mata da har yanzu ba a tantance ba, wacce aka ce ‘yar shekara 30 ta tsallake ta tsunduma cikin ruwa a gadar Third Mainland Bridge, jihar Legas a ranar Alhamis, 10 ga Nuwamba, 2022.

An tattaro cewa matar ta sauko daga wata taksi, ta nufi layin dogo na gadar ta fada cikin ruwa.

Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rahoton halin da ake ciki, ya ce an hada tawagar bincike da ceto domin nemo matar.

"Bayan isar LRT a wurin da lamarin ya faru, bincike ya nuna cewa wata mata 'yar shekara 30 (30s) ta nutse cikin tafkin Legas," in ji shi.

"Binciken da aka yi ya nuna cewa matar ta sauka daga wata taksi a kan gadar ta fada cikin tafkin,"

Shugaban LASEMA ya ce direban motar ya yi ikirarin cewa matar ta yi zazzafar zance da saurayinta kafin ta sauka daga motar.

Ya kara da cewa "'Yan LRT na hukumar kashe gobara ta jihar Legas, LASWA da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suna nan a kasa suna aiki tare domin neman matar."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN