Type Here to Get Search Results !

Wani sojan Najeriya ya harbe abokin aikinsa da ma’aikatan sa-kai har Lahira a Arewa maso Gabas


Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wani soja ya harbe ma’aikacin daya daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu da ke bayar da tallafin jin kai a yankin Arewa maso Gabas.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Nantip Zhakom ya kara bayyana cewa, sojan ya kuma harbi wani abokin aikinsa tare da raunata mataimakin matukin jirgin daya daga cikin jirage masu saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.

Har yanzu dai ba a san abin da ya kai ga harbin ba.  Zhakom ya ce;

“Rundunar Theater Command Operation HADIN KAI na nadamar sanar da jama’a wani abin bakin ciki da ya faru a daya daga cikin sansanin sojojin mu a yau.

“Wani soja ya harbe ma’aikacin daya daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu da ke bayar da tallafin jin kai a yankin Arewa maso Gabas har lahira.  Hakazalika sojan guda ya kashe wani soja tare da raunata mataimakin matukin daya daga cikin jirage masu saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.

“Nan take dakarun soji da ke wajen suka bindige sojan har lahira.  An kwantar da mataimakin matukin jirgin da ya jikkata yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Asibitin Shiyya ta 7.  An fara bincike kan lamarin da kuma matakan gyara da suka biyo baya cikin lamarin mai matukar nadama.

"Za a bayar da ƙarin bayani daga baya."

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies