Matasa sun kona gidajen wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kano
Wasu fusatattun matasa sun kona gidajen wasu da ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara biyar a kauyen Yantama dake karamar hukumar Doguwa a jihar Kano.
‘Yan sanda sun samu rahoto a ranar 28 ga watan Oktoba daga wani mazaunin karamar hukumar Doguwa, jihar Kano, cewa an yi garkuwa da dansa Hamza Harisu, mai shekaru 5, kuma masu garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa na naira miliyan 20.
Daga baya dai an tattauna batun kudin fansar zuwa naira miliyan biyar.
Bayan haka, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Abubakar Lawal, ya tara tawagar ‘Operation Restore Peace’ da za ta bi bayan masu garkuwa da mutane.
An kama wani matashi dan shekara 29 mai suna Ado Ibrahim a maboyar sa tare da wasu mutane uku.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce: “Wanda ake zargin ya amsa cewa shi kadai ne ya yi garkuwa da wanda aka sace din a ranar 27/10/2022 da misalin karfe 7 na yamma lokacin da duhu ya yi a wani daji da ke kusa da shi kuma ya shake shi har lahira.
Kiyawa ya ce daga baya tawagar jami’an ‘yan sanda suka gano gawar mamacin kuma an kai shi babban asibitin Doguwa domin duba lafiyarsa inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce bayan labarin ya bazu a cikin al’umma, wasu fusatattun matasa sun kona gidajen wadanda aka kama wadanda ke sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin bincike.