Hukumar Kwastastam NCS a jihar Kebbi ta jawo alherin N2b, ta kama buhun wiwi 284, buhun shinkafa 345, dilar gwanjo 139, duba sauran (Hotuna)

Hukumar Kwastastam NCS a jihar Kebbi ta jawo alherin N2b, ta kama buhun wiwi 284, buhun shinkafa 345, dilar gwanjo 139, duba sauran...


Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), reshen jihar Kebbi ta taimaka wajen fitar da kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida na sama da Naira biliyan 2 a cikin watan Oktoba a jihar Kebbi.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Kwastam na jihar Mr. Joseph O. Attah wanda ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Gwadangaji ya kuma bayyana cewa jami’an sa sun kama buhunan tabar wiwi guda 284, wanda aka fi sani da hemp India.

Lokacin da yake bayani kan nasarorin da rundunar ta samu a cikin watan Oktoba, Konturolan ya ce: “A tsawon lokacin da muke nazari, mun samar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 162,173,507 a matsayin kudaden shiga daga harajin shigo da kaya.  Wannan dai ba a taba ganin irinsa ba tun bayan bude iyakar Kamba.

Da yake magana kan ayyukan fasakwauri da kwace, Attah ya bayyana cewa, rundunar ta umurci jami’an sa da su kara sanya ido a cikin manya-manyan ciyayi da duk magudanar ruwa a jihar Kebbi.

Rundunar ta kuma kama surki 284 na tabar wiwi, da motoci 4 da aka yi amfani da su, da wasu motoci 2 da Honda civic.  motoci 1 da aka yi amfani da ita, da motar dizal da motar tipper 1.

Kazalika Konturolan ya ce rundunar ta kama dila 139 na kayan gwanjo da buhunan shinkafa 345 na kasar waje masu nauyin 50kg, da kuma lita 2,250 na man fetur da kwali 38 na mai da ake amfani da shi domin hasken fata watau bleaching, batura 80 na hasken rana, da dai sauransu.

“Kudin harajin da aka biya na kayayyakin da aka kama ya kai N78,562,125,” in ji Mr Attah Konturolan Kwastam na jihar Kebbi.

Kwamandan Hukumar NDLEA na Jiha, Sule Usman ya karbi surki 284 na tabar wiwi daga Konturolan Kwastam, ya yabawa Shugaban Kwastam, Mr. Joseph O.Attah bisa kyakkyawan aiki da shi da jami’an sa suke yi tare da.ba shi lambar girma na jakadan hukumar na yaki da miyagun kwayoyi a jihar Kebbi.

Latsa nan ka kalli Hotuna

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0zVSoz6GXGP6UvkqsJ5AbwD2ZSzou7BUujYt281uJJbuQaiNznoXtQFmXupgVX3qGl&id=100066486892301


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN