Maigida ya yi wa matarsa duka har lahira sakamakon karamin sabani


Rudunar yan sandan jihar Ogun ta damƙe wani magidanci ɗan shekara 45, Segun Omotosho Ebenezer, bisa zargin jibgar matarsa, Omotosho Olubukola, har tace ga garinku nan. Legit.ng ta wallafa.

Jaridar Daily Trust tace wanda ake zargin ya shiga hannu ne a maɓoyarsa ƙauyen Akinseku, Abeokuta, babban birnin jihar Ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna cewa mutumin ya narka wa matar Kwado na ƙarfe a kai kuma ya ji mata munanan raunuka a ilahirin jikinta.

An tattaro cewa wanda ake zargin, mai sana'ar Kafinta ya samu saɓani da mai ɗakinsa ne saboda ta ƙi yarda ta damƙa masa ragamar makarantar kuɗin da ta gina.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ranar Litinin. Yace yar uwar matar ta faɗa musu cewa Ebenezee ya ji wa matar raunuka kan karamin saɓani.

Wanda ake zargi da kansa ya garzaya da matar babban Asibitin tarayya FMC Idi-Aba Abeokuta domin kula da ita amma rai ya yi halinsa.

"Mijin bai sani ba, marigayyar ta tura sakon murya ga yan uwanta ta gaya nusu cewa Mijinta ya buga mata Kwaɗo a kai yayin da yake jibgarta, idan ta mutu su sani shi ne ya kasheta."

"Bayan jin sakon muryar, Magidancin ya gudu amma bayan samun rahoto DPO na caji Ofis ɗin Kemta ya umarci jami'ai su nemo mutumin duk inda ya shiga. Bincike ya nuna sun samu saɓani ne kan wata makaranta."

"Marigayyar ta gina makarantar da sunanta da mijin amma Magidancin ya nemi ya karɓe makarantar baki ɗaya ita kuma ta ƙi yarda, asalin sabanin da ya ja kullum yake jibgarta har wannan rana ta zo."

Mista Oyeyemi.

Ya ƙara da cewa kwamishina ya umarci a maida wanda ake zargi bangaren kisan kai na sashin binciken aikata manyan laifuka domin tsananta bincike da ɗaukar mataki, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa matashiyar mai suna Esther Paul, yar shekara 27 a duniya ta burma wa saurayinta wuƙa har rai ya yi halinsa a Layin Oba Amusa, Lekki.

Yan sanda sun gano wuƙar da Eather ta yi amfani da ita wurin aikata wannan ɗanyen aiki, sun ci gaba da bincike kan lamarin kafin zuwa Kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN