An tsinci gawar wata mata a wani dakin otel da safe bayan ta kwana da wani Alfa.
Matar mai suna Muinat mai shekaru 46 ta zo wurin ne a kan babur tare da wani Alfa Sule.
Sun sauka a gidan baÆ™i da ke Igbogbo a Ikorodu, jihar Legas, a ranar Juma’a, 18 ga watan Nuwamba.
Washegari , Asabar. A ranar 19 ga watan Nuwamba, manajan gidan bakin ya gano gawar matar a yayin da Alfa din ba ya nan, inda ya yi watsi da babur dinsa a harabar gidan baki.
Manajan gidan baki ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a Ikorodu.
Yan sandan sun halarci wurin kuma ba su sami wata alamar tashin hankali a kan matar ba, ko da yake sun tarar da kumfa yana fitowa daga hancin matar. Tuni dai aka ajiye gawar marigayiyar a dakin ajiye gawa na babban asibitin Ikorodu domin gudanar da bincike.
Rubuta ra ayin ka