Kotu ta sake soke zaben fidda gwani na Gwamnan Jihar Zamfara na PDP ta ce PDP ba za ta tsayar da kowane dan takara ba a zaben Gwamna 2023 a jjhar
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ta sake soke zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam'iyyar PDP wanda ya fito da Dauda Lawal-Dare a matsayin dan takararta a ranar Talata 8 ga watan Nuwamba.
Mai shari’a Aminu Bappa ya kuma ce jam’iyyar PDP ba za ta tsayar da kowane dan takara a zaben Gwamnan jihar a 2023 ba.
Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan da wata kotu ta soke zaben fidda gwanin da ya gabata wanda ya zabi Lawal-Dare sakamakon karar da Ibrahim Shehu da wasu ‘yan takara biyu suka shigar na kalubalantar sahihancin zaben fidda gwani.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI