Type Here to Get Search Results !

Dan Majalisar da ya yanke jiki a taron kaddamar da yakin neman zaben Tinubu ya rasu


Dan Majalisar Dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazabar Mushin II, Sobur Olayiwola Olawale ya rasu. Jaridar Aminiya a ruwaito.

Olawale wanda aka fi sani da Omititi, na cikin ‘yan siyasar da suka halarci taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yanke jiki ya fadi a wajen taron kuma daga bisani ya ce ga garinku nan.

Wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa ko a karshen makon da ya gabata suna tare da Olawale.

“Mun hadu ne a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon (GOS) a ranar Lahadi, inda muka gaisa. Kuma a wancan lokacin yana cikin koshin lafiya.

“Koma mene ne amma da alamu mutuwarsa na da alaka da hawan jini. Amma mutuwarsa ta girgiza mu.”

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies