Babbar magana: Mataimakin Kwamandan rundunar NSCDC ya yi batan dabo a jihar kudu


Bacewar mataimakin kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen jihar Bayelsa, Mista Raymond Gaadi, ya jefa rundunar cikin rudani.

Gaadi, wanda aka tura shi daga rundunar ta reshen jihar Enugu zuwa ga rundunar jihar Bayelsa domin gudanar da aiki a watan Afrilu, ya bace ne bayan an ba shi izinin tafiya jihar Enugu a watan Oktoba.

An ce yana samun matsala da wani abokin aikinsa, a cewar wata majiya ta iyali.

Ba za a iya tabbatar da ko an yi garkuwa da jami'in NSCDC, ko ya yi hatsarin mota ne, ko kuma ya fada cikin bala'in ambaliyar ruwa da ta kai kololuwa a lokacin da ya bace a wannan yankin.

Tsoron da ke cikin rundunar da dangin shi ne ko babban jami'in yana raye, saboda an ce lambobin wayarsa a kashe suke.

Babban yayansa mai suna Mista Terkura Gaadi, ya ce ya rasa kiran da dan’uwansa ya yi masa ne a ranar 22 ga watan Oktoba, kuma tun daga lokacin bai iya samunsa ba saboda wayoyinsa suna kara har zuwa ranar 30 ga Oktoba, inda duk layukan suka kashe.

Ya ce: “An dauke shi daga Enugu kuma ya koma aiki a Bayelsa a watan Afrilu, inda ya ke har ya bace a watan Oktoba.

“A gaskiya, ya kira ni a ranar 22 ga Oktoba, da misalin karfe 6 na yamma, amma na rasa kiran sa.

“Lokacin da na sake kira, ban samu amsa daga gare shi ba, don haka ne a ranar 30 ga Oktoba, wayoyinsa a kashe gaba daya ya zuwa yau.

“A lokacin ne muka fara jin cewa tabbas wani abu ya same shi.

“Ni da kaina na yi magana da kwamandan NSCDC a jihar Bayelsa kuma ta shaida min cewa suna kokarin gano inda yake.

“Lokacin da na ziyarce shi a watan Mayu, ya shaida min cewa ya samu matsala lokacin da ya ci gaba da aiki a jihar Bayelsa.

“Mun riga mun rubutawa babban sufeton ‘yan sanda da kuma kwamandan NSCDC.  Su nemo inda dan uwanmu da ya zo yiwa kasa hidima a jihar Bayelsa yake.  Muna so mu gan shi a raye.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN