Lamarin ya faru ne a yankin Babale da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
An gano gawar ne a ranar Juma’a kuma aka binne gawar a ranar Asabar.
Wani mazaunin garin da ya so a sakaya sunansa ya ce: “Lamarin ya faru ne a Kururuwan ka banza, dajin mai kauri tsakanin Zakaliyo da Babale.
“Yaron mai shekaru tsakanin 19 zuwa 21, ya yi batan dabo tsawon kwanaki hudu.
“A rana ta bakwai da ake bincike, an tsinci gawar yaron a daya daga cikin duhuwar Kururuwan ka banza tare da cire masa idanu biyu, da kuma azzakarinsa.
"An binne gawar a wurin da suka tsinci gawar, saboda gawar ta ruba."
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce: “Rundunar ta na sane da abin da ya faru a Babale. DPO na yankin da tawagarsa suna aiki a kai don bankado wadanda ke da hannu a wannan aika aika.
“Kwamishanan ‘yan sanda ya fusata da irin wannan lamari kuma ba za a bar wani dutse ba wajen gurfanar da wanda ya aikata laifin.”
Rubuta ra ayin ka