Zaratan hadin gwiwan jami'an tsaro sun kubutar da DPO na Birnin Gwari da yan bindiga suka sace watanni uku da suka gabata
DPO na Birnin Gwari da Yan bindigan suka sace watanni uku da suka gabata, CSP Sani Mohammed Gyadi-Gyadi, ya kubuta.
Rahotannin PRNigeria na cewa hakan ya faru ne sakamakon wani kutse karkashin kasa sakamakon ayyukan sirri tsakanin jami'an tsaro da ya kai ga ceto babban jami'in na Yan sanda.
Sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani ko an rasa rai a wanan aikin ceto da jami'an suka yi wanda tuni masana harkar tsaro a Najeriya suka yaba wa nassarar aikin.