Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai wa ayarin motoccin babban Malamin addini a Najeriya hari, sun kashe mutum 7 har da yan sanda


Yan bindiga sun kai wa ayarin motoccin Apostle Johnson Suleiman hari a kanyar Benin-Auchi, Jihar Edo, a ranar Juma'a sun kashe mutum bakwai ciki har da yan sanda uku.

The Punch ta tattaro cewa Suleiman ya dawo daga tafiya ne a kasar waje yana hanyarsa ta zuwa Jihar Edo inda yan bindigan suka kai masa hari a kusa da Auchi a jihar.

Yayin harin, yan bindigan, an rahoto sun bude wa ayarin motoccin wuta, sun kashe yan sanda uku masu tsaronsa da wasu mutane hudu da ba a gano su wanene ba.

Lauyan Suleiman, Samuel Amune, wanda ya tabbatarwa The Punch harin ya ce, faston ya dawo daga wani shiri ne da ya tafi a Tanzania, ya kuma sha da kyar.

Ya ce:

"Yana dawo daga tafiya ne ya kuma kai Auchi lokacin da wasu makasa suka afka masa. Yan sanda masu tsaronsa uku da wasu sun mutu. Ya yi tafiya kuma ya dawo kenan daga Tanzania inda ya halarci wani shiri a shekaran jiya.

"Yana hanyarsa ta komawa Auchi ne lokacin da yan bindigan suka kai masa hari kusa da Sabingida zuwa Warake, Auchi na da iyaka da Warake. Ya wuce Warake ya fara shiga Auchi harin ya faru."

Wani kwararre a bangaren tsaro, Dickson Osajie, ya yi suka kan rashin tsaro a jihar, ya ce harin ya faru da rana tsaka.

Ya ce:

"Sun kai masa hari (Suleiman); mutum bakwai har da yan sanda sun mutu. Ba tsaro a kasar; mutanen mu suna yawo da bindiga a tituna ba a gane su ba. Abin damuwa ne."

Martanin yan sanda

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan Edo, Chuidi Nwabuzor ya ce:

"Ban dade da jin labarin ba; amma ba zan iya tabbatarwa ba. Bari in tuntubi DPO da ke kula da yankin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN