Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da damuwar da 'yan Najeriya ke ciki na bashin da ake bin kasar.
Tinubu ya bayyana cewa, da ace cin bashi laifi ne, da yanzu haka ilahirin kasar Amurka ta zama magarkama saboda tudun bashi, rahoton TheCable.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba yayin ayyana manufofinsa gabanin babban zaben 2023.
Tinubu ya bayyana cewa, shi da abokin gaminsa, Kashim Shettima sun shirya daukar hanya dodar na gyara Najeriya tun ranar farko da suka lashe zabe.
Ya kuma bayyana cewa, kasar nan na bukatar mutanen dake da gogewa a fannin magance matsalolin tsaro, kawo ci gaba da daukaka dajararta.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI