Yanzu yanzu: Ana fargaban Safeto Sanusi Kangiwa dogarin Khadi Saddiq ya rasu a hatsarin mota a gadar Dukku, Birnin kebbi bayan motarsa ta tsunduma cikin ruwa



Rahotanni na cewa ana fargaban Safeto Sanusi Kangiwa ya rasu sakamakon hatsari da ya rutsa da shi da wani mai babur a gadar Dukku da ke kan hanyar kauyen Makera  ranar Laraba 5 ga watan Oktoba.

Safeto Sanusi Kangiwa shi ne dogarin babban Alkali Khadi Saddiq Usman Muhktar na Ma'aikatar shari'a a jihar Kebbi. 

Bayani na cewa Sanusi tare da wani abokinsa Dan sanda, suna cikin motarsa kan hanyarsu ta dawowa daga sayen itacen girki, sai wani mai babur ya gitta masu a daidai gada na uku kafin tsaunin Dukku, lamari da ya sa mai babur ya mutu nan take, yayin da motar Safeto Sanusi ta tsunduma cikin ruwan rafin Dukku kuma ta nutse tare da shi a cikin motar. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare.

Majiyarmu ta ce an sami ceto abokin Sanusi da suka tsunduma cikin ruwa a motar, sai dai har yanzu ba a gano Sanusi ba, kuma ana fargaban ya mutu a cikin motar a cikin ruwa.

Kazalika majiyarmu ta ce an nemo gwanayen ninkaya daga garin Tarasa da ke makwabta da rafin Dukku domin nemo Sanusi, sai dai har karfe 4 na asuba ya yi ba a gano shi ba. Lamari da ya sa ake kyautata zaton cewa Allah ya yi wa Sanusi cikawa a wannan ibtila'in. 

Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce kawo lokacin rubuta wannan rahotu DPO na Yan sanda reshen runduna ta garin Birnin kebbi tare da jami'ansa da sauran jama'a na kokarin fitar da motar tare da gawar Safeto Sanusi daga cikin ruwan rafin. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN