Yadda wani mutum ya kaura wa budurwarsa cikin shege ya kuma kashe jariri dan mako 3 da ta haifa

Yadda wani mutum ya kaura wa budurwarsa cikin shege ya kuma kashe jariri dan mako 3 da ta haifa


An kama wani mutum da abokinsa a Nasarawa bisa laifin kashe yaronsa mai sati uku

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kama wasu mutam biyu, Abdulkadir Ahmed da Hassan Sabo maza da shekaru 40 a Ungwan Maina da ke garin Lafia bisa zargin kashe wani yaro dan mako uku da haihuwa.

Binciken farko kan lamarin kamar yadda mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan juhar, DSP Ramhan Nansel ya tabbatar, ya nuna cewa a ranar 11 ga watan Oktoba, baban wanda ake zargin, Abdulkadir Ahmed ya bukaci abokinsa Hassan da ya kama mahaifiyar marigayin zuwa shagonsa da ke daura da gidan gyaran hali, Lafia a karkashin hukumar. dalilin neman sulhu kasancewar mahaifiyar jaririn budurwarsa ce wadda ya samu ciki amma ya sallame ta bayan ta gaya masa tana da ciki.

“Da isowarta shagon, Abdulkadir Ahmed ya shigar da yaron cikin shagonsa yayin da Hassan Sabo ya hadata da ita a waje, sai ga yaron ya yi kururuwa, ya yi shiru.

Nan take Abdulkadir Ahmed ya fito daga shagon, mahaifiyar ta tambayi dalilin da yasa yaron ya yi kururuwa amma aka ce yaron ya kwanta. Ba ta gamsu ba, sai ta garzaya cikin shagon ta gano gawar yaronta babu rai yayin da nan take masu laifin suka zagaya da babur.” Inji Nansel.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, an sanar da ‘yan sandan, sannan aka garzaya da gawar zuwa asibitin kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya, inda aka tabbatar da mutuwar yaron, daga bisani kuma aka ajiye gawar a dakin ajiye gawa.

Nansel ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi a kan masu laifin.

"Ana ci gaba da gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar, bayan haka, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu," in ji Nansel.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN