Gwamnatin Zamfara ta rufe NTA Gusau, Prime FM, da sauran su, duba dalili
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar a Gusau ranar Asabar.
Kwamishinan ya ce sauran kungiyoyin yada labaran da aka sanya wa takunkumi sun hada da Gamji TV da Gamji FM da kuma Al umma TV wadanda ke zaman kansu.
Dosara ya ce kwamitin tsaro na jihar ya amince da rufe tashoshin.
A cewarsa, an umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya kama tare da gurfanar da jami’an ofishin da lamarin ya shafa da aka kama suna karya dokar.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI