Yadda mutum tara yan gida daya suka yi mutuwar gaggawa a wata jihar Arewa

Yadda mutum tara Yan gida daya suka yi mutuwar gaggawa a wata jihar Arewa.


Mutane tara ‘yan gida daya ne suka mutu a wani yanayi na ban mamaki a garin Nagazi da ke karamar hukumar Adavi a jihar Kogi
.

Wannan lamari na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan uwa hudu suka mutu bayan sun ci abinci ‘amala’ a garin Mopa da ke karamar hukumar Mopa-Amuro ta jihar Kogi a karshen mako.

An tattaro cewa lamarin wanda ya faru da yammacin ranar Litinin, 3 ga watan Oktoba, a gidan wani Alhaji Ozankuroko, ya ga wasu ‘yan uwa guda biyar sun mutu a wuri guda kafin a garzaya da wasu hudu zuwa asibiti.

Sauran hudun daga baya sun mutu a asibitin da ba a bayyana ba a yankin.

Wata majiya daga dangin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kama mahaifin wadanda suka mutu yayin da mahaifiyar ke ci gaba da karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Ya ce har yanzu ba su san ainihin musabbabin mutuwar ba amma suna zargin gubar abinci ko kuma wani hari na ruhaniya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, William Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels da ke Lokoja a ranar Talata. 

Hukumar Yan sanda ta PPRO ta ce rundunar tana aiki tukuru domin gano musabbabin mutuwar, inda ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN