Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban matasan jam’iyyar APC a jihar Najeriya
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Lucky Okechukwu, shugaban matasa na jam’iyyar All Progressives Congress a karamar hukumar Igboeze ta kudu a jihar Enugu.
Punch ta ruwaito cewa an harbe Okechukwu ne a daren ranar Asabar 8 ga watan Oktoba a unguwar Unadu da ke garin.
Wani jigon jam’iyyar da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce;
“Eh, gaskiya ne. Ban san ainihin sunansa ba amma mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe shi a daren jiya. Idan jam’iyyar na son yin magana kan lamarin, to ko shakka babu za ta fitar da sanarwa a kan hakan.”
Rubuta ra ayin ka