Wani mutum ya rusa gidajen da ya gina wa matarsa da mahaifiyarta bayan ta yi watsi da shi saboda wani mutum, duba yadda ta faru
Wani dan kasar Malawi mai suna Francis Banda ya rusa gidajen da ya gina wa matarsa da mahaifiyarta bayan matar ta rabu da shi saboda wani mutum. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
A wani faifan sauti da aka watsa a shafukan sada zumunta, Banda ya ce shi da matarsa sun yi aure shekara 13 kuma suna da ‘ya’ya uku, kamar yadda Malawi 24 ta ruwaito.
Ya kara da cewa a lokacin aurensu ya yi nasarar gina gidaje biyu daya na matar daya kuma na mahaifiyarta a kauyen uwargidan.
A cewar Banda, matarsa ta fara dangantaka da wani mutum, kuma kwanan nan ta bar gidansu ta koma wajen mutumin.
A wani lokaci Banda ya yi ƙoƙarin yin magana da matan a wayar salula, amma sai sabon mutumin ya amsa kiran wayarta .
Hakan ya fusata Banda ya yanke shawarar rusa gidajen da ya gina wa matar da mahaifiyarta a kauyensu.