Type Here to Get Search Results !

Rikicin Hausawa da ƙabilu a Sudan ya kashe mutum 200


Jami'ai a Sudan sun ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin ƙabilanci da ake yi a kudancin kasar tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Berta ya ƙaru zuwa 200.

BBC ta ruwaito wani shugaban al'umma a Jihar Blue Nile ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyuwa uku, inda ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su taimaka wajen binne gawarwakin wadanda suka rasu.

Rahotanni na cewa ana rikici tsakanin Hausawa da Berta ya ɓarke ne kan gonaki.

A jiya Juma'a aka sanya dokar ta-ɓaci ta tsawon kwana 30 a fadin jihar ta Blue Nile.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies