Wani malamina ya ce muryata na tayar masa da sha'awa''


Wata daliba a Najeriya ta bayyana irin halin da dalibai mata ke shiga na fuskantar cin zarafi na lalata daga malamansu da nufin ba su damar cin jarrabawa ko wani ci-gaba a karatunsu.

Dalibar ta bayyana wa BBC irin yadda wani malaminta a jami’a ta ce ya ci zarafinta da neman ya yi lalata da ita da alkawarin taimaka mata a karatunta, inda ta ce ya bayyana mata cewa muryarta tana tayar masa da sha’awa;

‘’Ni wannan abin ya faru da ni farko a University inda wani malamina ya yi harassing dina by saying that irin voice dina was sexy, yana tayar masa da sha’awa kuma yana so na taimake shi na kashe mai kishirwarnan, shi ma zai taimake ni ta hanyar sawa na ci dukkanin courses dina a makaranta.’’

Dalibar wadda ba a bayyana sunanta ba da kuma inda take domin kare sirri da mutuncinta ta gaya wa BBC cewa, wannan ta’ada ta yadda malamai ke neman dalibai tana faruwa kusan a dukkanin matakai na manyan makaruntun gaba da sakandire a Najeriya, ba wai sai jami’a ba.

Ta ce saboda ko ita ma sheda ce domin ya faru da ita a matakai uku na manyan makarantun gaba da sakandire, kama ‘’daga university, college of health, federal college da kuma Polytechnics, saboda haka mutum ba zai iya cewa takamaimai ga inda abin ke faruwa ba yana faruwa kusan a ko’ina’’ in ji ta.

Matashiyar ta ce dalibai mata na fuskantar wannan matsala wasu ma ba su san yadda za su yi ba domin suna samun kansu a yanayi na cutar damuwa saboda ba wanda zai taimake su.

Ta kara da cewa wasu matan sun rasa budurcinsu wasu sun rasa mutuncinsu da kimarsu a matsayinsu na ‘ya’ya mata duk ta dalilin wannan ta’ada da malaman makaranta ke neman dalibansu.

Dalibar ta kuma kara da cewa abin yana faruwa ba sau daya ba ba sau biyu ba ba kuma za a iya ware wani rukuni na mata a ce a kansu kawai yake faruwa ba, yana faruwa ne a makarantun gaba da sakandire.

Inda ta ce ‘yan mata da dama da ke manyan makarantu, a kashi dari kusan kashi saba’in sun gamu da wannan matsala. 


Kasancewar ana ta’allaka wannan ta’ada inda malamai ke neman dalibai a manyan makarantu musamman jami’o’i, da neman cin jarrabawa, wata daliba ta ce abin bai tsaya ga dalibai marassa kokari ba.

Domin ta ce ita tana da kokari kuma wannan kokari nata ne ma ya sa har malaminsu a jami’a ya santa kuma ya karkata hankalinsa wurinta da neman yin lalata da ita.

Ta sheda wa BBC cewa wata rana bayan sun gama karatu ne sai shugaban dalibai na ajinsu (monitor) ya gaya mata cewa babban malamin da ke kula da karatunsu, yana son ganinta a ofis, inda ta je ta same shi.

Dalibar ta ce bayan ta je ofishin ne sai malamin ya tattauna da ita game da karatunta kasancewar ya ga irin kokarin da take da shi inda ya shawarce ta da ta kara dagewa.

Kuma ya tambaye ta ko tana da wata matsala, inda ta ce babu, sai dai ya ce a duk lokacin da ta gamu da wata matsala ta je ta gaya masa.

Ta yi bayanin cewa bayan kwana biyu da wannan zama sai ya kira ta ta waya ya ce ba ya ganinta, inda ta sheda masa cewa ba ta da karatu ne shi ya sa.

Ta ce daga nan ne ya ce mata, to a duk lokacin da ta shigo makarantar ta zo yana nemanta.

Matashiyar ta ce bayan da ta shiga makarantar ta je ofishinsa, da suka gaisa, ‘’ Bayan mun gaisa cike da mamaki sai na ga ya tashi ya tafi kofa ya rufe sai na tsaya dai in ji me zai ce.

‘’Bayan ya rufe kofar, a’a, abin da ban taba tunani ba a wannan lokacin shi ya faru, shi ne na ga mutumin ya fara tahowa inda nake kafin na yi magana na ce ma wani abu har ya rike hannuna, nake ce masa meye haka?’’ In ji ta.

Daga nan ta yi bayani da cewa, ‘’Ya ce min ai ba komai me ya sa nake abu kamar yarinya ne bayan na shiga jami’a?’’

Wannan abu ya faru da ni shekarata ta farko bayan na shiga jami’a a cewarta.

‘’Ya ce ai ni babbar yarinya ce yanzu tun da na shiga jami’a, sai na ce ni ba babbar yarinya ba ce kuma ni ba abin da iyayena suka turo ni na yi ba kenan, kafin na sani ma ya fara shafa min fuska.’’

Dalibar ta ce har sai da ta kai ya fito fili ya gaya mata abin da yake so ya yi da ita, inda daga nan ta fara kuka tana karkarwa.

Ta ce ita yadda ta dauke shi kamar uba ba ta yi tsammanin zai yi mata haka ba, ta gaya masa cewa idan bai kyale ta ba za ta yi ihu, daga nan ne ta samu ta fita bayan ya yi mata barazana cewa za ta gani a kwaryarta.

Matashiyar ta ce tun daga sannan ta fara ganin sakamakonta ya fara raguwa na jarrabawa a makarantar.

Duk da cewa malamin ya ci gaba da kiranta ta waya domin ta ba shi damar abin da yake son ya yi da ita, inda abin ya fara damunta kasancewar ba ta san wanda za ta nufa da maganar ba har ya kai ga ta sauya makaranta a karshe.

Sai dai kuma ta ce ko a sabuwar makarantar da ta koma ba ta da tabbacin hakan ba za ta faru da ita ba.

Amma ta ce a yanzu a shirye take domin ta kara sanin kanta da kuma wannan barazana.

Ita dai wannan matsala wadda malamai ke neman dalibai a manyan makarantu musamman jami’o'i a Najeriya da wasu kasashe aba ce da ta zama ruwan dare, inda ta kai har a wani lokaci a baya BBC ta gudanar da wani bincike na sirri ta yi rahoton da ya kai ga korar wasu malamai a wasu jami’o’in Najeriya da Ghana.

Ko a cikin kwanakin nan Shugaba Muhammadu Buhari ya ambato nau’i daban-daban na irin wannan matsala da ya danganta ta rashawa a jami’o’in kasar.

Rahotun BBC 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN