Abin da ya sa masana ke ganin mawakan zamani na wulakanta rubutun Hausa


 Daga baƙon marubuci, Dr Muhammad Suleiman Abdullahi, malami a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero, Kano. 

Waƙa tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin isar da saƙwanni da taskace harshe da sanya annashuwa da karsashi ga zukatan masu sauraro, musamman idan aka sami zaƙwaƙuran da suke aiwatar da waƙoƙin ta hanyoyin da suka dace.

A ɗaya ɓangaren kuma, rubutu hanya ce ta bayyana tunani da muradun zuciya, ta yadda ko da ma'abocin wannan tunanin ba ya nan, wani zai iya gane wannan tunani har ma ya amfana daga abin da wannan tunani da fasaha suka ƙunsa.

A fuska ta nazari, akwai waƙoƙin da aka fi sani da rubutattun waƙoƙi. Su irin waɗannan waƙoƙi sun sha bamban da waƙoƙin baka saboda masu aiwatar da su galibi sai sun rubuta su (to a nan gizo yake saƙa) sannan suke aiwatar da su.

Akwai sama da dokoki da ƙa'idoji sama da guda ɗari (100) da suka shafi yadda tsarin rubutun Hausa yake, amma ga alama, waɗanda suke rubuta irin waɗannan waƙoƙi ba su ma san ko da kashi goma cikin waɗannan ɗarin ba.

Don haka za ka ga an rubuta wani abu wanda idan mutum bai yi a hankali ba, sai wannan abu ya sabbabawa mai karatu rashin fahimta ko mummunar fahimta ko ma ya lahanta tunani bakiɗaya.

Masu rera irin waɗannan waƙoƙi, sukan rubuta su, ko kuma su rubuta sunayen taken waƙoƙin, amma abin mamaki, a sunan da bai wuce kalma biyar ba, sai ka ga an sami kurakurai da yawa.

Irin waɗannan waƙoƙi da kuma mummunar hanyar da ake rubuta su, takan yaɗu kamar wutar daji, tare da cewa a kan kuskure rubutun yake, wani lokaci har ma su sake su a shafukan sadarwa, kamar su Yutub ko Fesbuk da su Tuwita da makamantansu.

Waƙoƙin Ado Gwanja

Ado Gwanja
ASALIN HOTON, ADO GWANJA

Akwai misalai da dama na irin wannan taƙadarin tsarin rubutu na taken waƙoƙin zamani, waɗanda za a kawo su a nan, tare da bayyana irin kurakuran da suke ƙunshe a cikin wasunsu.

Misali a wata waƙa ta Ado Gwanja wadda ta yi suna a tsakanin matasa a 'yan kwanakin nan, wadda ya sa wa suna, kuma aka rubuta sunan waƙar da "Chass", duk da cewa taken waƙar kalma ɗaya ne kawai, amma ba a rubuta shi daidai ba.

Kalma ɗaya fa! A Daidaitacciyar Hausa ba a amfani da baƙin [ch] wanda yake a Ingilishi a matsayin baƙin [c] na Hausa.

Sai dai fa a wasu ɗaiɗaikun wurare da tasirin mulkin mallaka ya yi mana kaka-gida. Don haka dai, kamata ya yi taken wannan waƙa a rubuce ya zama "Cass" ba "Chass"!

Sannan abin da ya faru na samuwar "ss" a ƙarshen kalmar "Cass", wata doka ce da za a iya tattauna ta a ilimin Tsarin Sauti na Hausa.

Waƙoƙin Umar M Shareef

A wata waƙar kuma ta wani mawaƙin mai suna Umar M Shareef, wadda aka yi wa taken "Kibani Soyayya", nan ma akwai gaggan kurakurai da yawa.

Misali, a Hausa ba wata kalma "Kibani" amma ga shi an yi amfani da ita a nan, kuma wai Hausar ake yi.

To amma daga cikin abin da ake faɗa a cikin waƙar, sai muka gano ashe wai so suke su ce "Ki ba ni" wanda kuma waɗannan kalmomi ne guda uku masu cin gashin kansu a tsarin Nahawun Hausa.

Umar M Shareef
ASALIN HOTON, UMAR M SHAREEF FACEBOOK

Wakilin Suna ne a farko, sai Aikatau da kuma wani Wakilin Sunan. Ko me ye dalilin da ya da marubucin taken waƙar ya rubuta "Kibani"? Wannan kuma shi ya sani.

Haka nan, akwai wata waƙar ta shi Umar M Shareef ɗin wadda aka rubutawa taken "Nafada", wadda har zuwa yanzu dai ban gano me yake so ya rubuta ba, domin ban saurari waƙar ba.

Waƙar Lilin Baba

A wata waƙar kuwa ta Lilin Baba da Ummi Rahab wadda aka yi wa taken "Zanyi Wuff", a nan ma za a iya cewa ba wata kalma a Hausa da ya dace a rubuta ta da "Zanyi".

To amma a lokacin rerawa suna faɗar "Zan yi" ne, amma a rubuce, sai suka rubuta wani abu daban mara ma'ana.

Hamisu Breaker

Ita kuwa wata waƙa ta Hamisu Breaker, wadda aka rubuta takenta da "Yadda Kunne Yaji", wato a nan dole masanin ƙa'idar rubutu da sauran ɗaliban harshe, musamman ɗaliban Hausa waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne, su shiga tashin hankali.

Hamisu Breaker
ASALIN HOTON, HAMISU BREAKER FACEBOOK

Domin ba Hausawa ba ne kawai suke karanta irin waɗannan rubuce-rubucen. Abin da zai fara zuwa zuciyar mai karatu shi ne wai shin me ye alaƙar kunne da yaji?

Kunne dai wata kafa ce da mutane suke jin magana da ita. Shi kuwa yaji, wani sinadari ne da ake sa wa a abinci domin inganta ɗanɗano.

To a nan an haɗa kunne da yaji... Ka ga ai sai tafiya asibiti. To amma daga baya sai muka fahimci ana so a rubuta "Yadda Kunne Ya Ji" ne, amma saboda ba a damu da sanin ƙa'idar ba, kawai sai aka rubuta abin da aka ga dama, kuma wannan zai iya zamewa masu koyo babbar matsala.

Haka ma wata waƙar ta shi Hamisun da aka rubuta takenta da "Nayi Saa", wanda duk waɗannan kalmomin guda biyu, babu su a Hausa.

Abin da suke so su rubuta, kamar yadda suka faɗa a waƙar, shi ne "Na Yi Sa'a"!

"Sai dake" ta Hamisu Breaker ma ba daidai ba ce. Daidai ɗin shi ne "Sai Da Ke".

Garzali Miko

Shi ma Ghazali Miko da Rakiya Musa haka suka tafka nasu kuskuren a wajen rubuta taken tasu waƙar, inda suka yi amfani da wata kalma wadda babu ita a harshen Hausa, alhali kuma waƙar Hausa suke yi.

Sun rubuta "Sona Amana" a maimakon "So Na Amana".

Waƙar Garzali Miko ta "Badan dake ba", ita ma kuskure aka rubuta. Daidai ɗin shi ne a rubuta "Ba Don Da Ke Ba".

Haka ma waƙarsa ta "Abun wani sirine" kamata ya yi a rubuta "Abin Wani Sirri Ne".

Wasu mawakan

Auta MG Boy kuwa, kalmomi ne guda huɗu cur, ya haɗe su ya mayar da su guda biyu kacal, kuma ya rubuta hakan abinsa.

A maimakon a rubuta "Ina Ji Da Ke" wanda shi ne daidai, sai aka rubuta wani gwarantaccen rubutu wai "Inaji Dake", wanda wannan ba mutunci ba ne.

Inaji Dake – Auta MG Boy 2022

https://youtu.be/B1h5dFJh6yA

A wata waƙar ta Sadiq Saleh, wai ita "Zanayo Shagwaba", wato a nan rashin daidai ɗin ma har ya yi yawa, domin ba wata kalma da aka rubuta daidai. Kamata ya yi a rubuta "Za Na Yo Shagwaɓa"!

Zanayo Shagwaba (Abin ya motsa remix  – Sadiq Saleh

https://youtu.be/_RagGuN0T6M

Ita ma waƙar "Soyayya ce ta Hadamu" ta Mg Boy, kamata ya yi su rubuta "Soyayya Ce Ta Haɗa Mu", ba kamar yadda suka rubuta ba.

Soyayya ce ta Hadamu – Auta Mg Boy 2021x

https://youtu.be/VT0mXu-8evo

Ga wasu sauran waƙoƙin da su ma duk ba a rubuta su daidai ba. "Ayimini Aure" ta Auta Mg Boy, kamata ya yi a rubuta ta kamar "A Yi Mini Aure".

Ayimini Aure – Auta Mg Boy da Rakiya Musa – 2020

https://youtu.be/mbOgGbn4vrg

Sauran waƙoƙi

Lilin Baba
ASALIN HOTON, LILIN BABA FACEBOOK

Akwai wasu waƙoƙin da dama da mai karatu ma da kansa idan ya duba, zai tabbatar da cewa lallai waɗannan mawaƙa kawai rubutawa suke yi ba tare da sun bi dokoki da ƙa'idojin rubutun Hausa ba.

Duk da cewa a wasu lokutan za su iya cewa ba su suke rubutawa ba, to amma wannan ba hujja ba ce, domin suna tutiyar cewa waƙoƙinsu ne, don haka dole su ɗauki duk abin da ya biyo baya, mai kyau ko akasinsa.

Haka kuma, ya kamata in dai mutum so yake ya inganta abin da yake yi, to ba da ka kawai ake yin abubuwa ba, akwai buƙatar a tuntuɓi masana domin su dinga dubawa don ganin an ƙara inganta wannan harshe na Hausa.

Ya kamata masu irin waɗannan rubuce-rubuce su sani, akwai masu karanta su da yawa, wasu daga ƙasar Hausa wasu kuma daga sauran sassan duniya.

Rashin inganta rubutun yana ba wa masu koyo matuƙar wahala wajen ganewa.

Don haka, a ƙarshe, nake shawartar dukkanin marubuta da su dan inda ya kamata a haɗe kalma da kuma inda ya kamata a rabata, da kuma dalilan da suke sa wa a yi hakan.

Sannan kuma dole ne a dinga amfani da baƙaƙe masu lanƙwasa, kamar su "ƙ" da "ɓ" da "ƙy" da makamantansu.

Sannan kuma a san baƙaƙen da ake amfani da su da na waɗanda ba a amfani da su. Duk waɗannan za su taimaka wajen inganta rubutu a harshen Hausa.

Ko za ku iya tantance matsalolin da suke cikin taken waɗannan waƙoƙin da aka kawo a ƙasa?

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN