Hukumar NDLEA ta kama Hakimin kauyen Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sakkwato Abubakar Ibrahim da surki 991,320 na daurin tabar wiwi da kuma kilo 1,251 na wiwi da khat.
Hakazalika hukumar ta kuma kama kilogiram 46.637 na meth, da kuma hodar iblis watau cocaine. Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kwato tabar heroin a jihohi bakwai.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Hakimin na hannun hukumar yayin da take ci gaba da gudanar da bincike.
Rubuta ra ayin ka