Miyagu sun aikata wa dan sanda mugun aiki, sun dauki wani muhimmin abu suka gudu - ISYAKU.COM


A safiyar ranar Asabar ne dai aka samu barkewar bala’i a titin Egerton da ke karamar hukumar Calabar ta Kudu, biyo bayan kashe wani dan sanda mai suna Sajan, Peter Ikwen da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi. Vanguard ta ruwaito.

Jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sanda, SP Irene Ugbo, wadda ta tabbatar wa jaridar Vanguard wannan mummunan al’amari ta wayar tarho, ta ce abin takaici ne kuma ba za a lamunta shi ba.

“A bayanin da nake samu da misalin karfe 8:00 na safiyar yau, ya fito ne daga fadar Obong inda aka tura shi aiki, amma yana aiki da sashen Atakpa, kafin a harbe shi.

“A kan hanyarsa ne maharan suka tare shi kusa da kwandon shara da ke kusa da fadar Obong suka harbe shi.

“Sun kuma kwace bindigar sa a cikin haka, muna jajanta wa iyalan marigayin, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samu wadanda suka aikata wannan abu, za mu fatattake su, doguwar hannun doka za ta kama su.  su,” in ji ta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN