Maza fiye da 500 sun yi lalata da ni don na samu damar zuwa Turai'


"Cikin masu yin lalata da mu a garin Maghnia da ke kasar Aljeriya har da wadanda suke da cutar HIV, wasu ma sun mutu a kan idanunmu".

Yadda wata matashiya 'yan asalin Najeriya ke tuna irin cin zarafi da wahalhalun da ta fuskanta a kan hanyarta ta tafiya ci-rani nahiyar Turai kenan. BBC Hausa ta ruwaito.

Mun sakaya sunan wannan matashiya muka sa mata suna Ada saboda wannan labarin.

Ta fada tarkon masu safarar mutane ne a 2016, lokacin tana ‘yar shekara 20.

Aikin gyaran gashi take yi a Jihar Delta, kuma mutumin da ya yi mata romon-baka ya nuna mata cewa yana da 'yar uwa da take gyaran gashi a Turai, kuma Turawan suna son yadda 'yan Najeriya suke yaran gashi sosai.

Wannan shi ne asalin abin da ya sanya Ada barin gida, da zummar za ta je Turai kai-tsaye domin ci gaba da sana'ar da take yi a Najeriya.

Amma ta kwana da sanin cewa hanyar kasa za su bi su tafi ba jirgi za su hau ba, domin kuwa ko fasfo ba ta da shi.

Cikin motar awaki aka zuba mu daga Nijar


"Tafiyarmu ta Nijar ta fara — daga Nijar ne mun bi ruwa mun bi rana, mun shiga sahara kuma mun kusa wata guda cikinta.

"Wani buzu ne ya kwashe mu a motarsa, muka dauki hanya ban da tsayin kwana da tuni na mutu a wannan saharar, motar da muka shiga muna da yawa mun kai 20 maza da mata a kwance a but din motar."

"A kwance muke kafada-da-kafada, wasu mutane da ke cikin saharan sun tsayar da mu, suka tambayi direban su waye a cikin motar, direban ya ce tinkiyoyi ne a ciki, a raina na ce ‘ohh wai ni ce tinkiya.’”

"Da yake motar a lillube take da tamfol, sai suka ce a cire shi su gani, kamar shi buzun da ya dauko mu yana da asiri a jikin zobensa, yana mirzá zoben sai ya bude ga mu dai a ciki amma tinkiyoyi suke gani,” in ji Ada .

Ada ta ce a karshe sun samu shiga Aljeriya zuwa wani gari da ake kira Oran.

Masu HIV na cikin wadanda suka rika yin lalata da mu


Ba Ada ce kadai ta fuskanci irin wannan tashin hankalin ba, akwai daruruwan matasa da ke irin wannan tafiya daga nahiyar Afrika, babu wanda ke tsira daga maza har mata.

A Aljeriya akwai wata tashar da ake jibge 'yan ci-ranin da suke bin hanya domin shiga Morocco, za su jira har sai an saci numfashin jami'an lura da shige da fice sai a tsallaka da su Rabat.

An ajiye su Ada a wannan wuri kimanin watanni biyu, kuma a cikin wasu dakunan tamfol suke kwana, babu dare babu rana maza ne kawai ke tsallakowa suna zabar matan da za su je su kwanta da su.

"Ni dai ba a min wannan cin zarafin ba saboda mu 'yan matan Oga ne, ya fada tun kafin mu karaso cewa kada wanda ya kusance mu, mun huta a wurin, abin da ba a yi a wajen kamar sanya gajeren wando da karamar riga mu duk sai da muka yi, babu wanda ke taba mu."

"Cikin wadanda suka rika neman matan da ke wurin akwai wadanda ba su da lafiya, ana zargin HIV ce da su, a cikinsu akwai wadanda muna wannan wurin suka mutu, ba ruwansu da amfani da kororon roba, in ma kin yi ciki babu ruwan kowa,” in ji Ada.

"Yadda na fara karuwanci a Morocco"


Da aka kai ni Morocco sai na nemi na kama gabana a Casablanca, sai aka ce ai ba ni da 'yancin tafiya saboda ana bi na bashi matar da ta biya kudi aka yi jigila da ni daga Najeriya zuwa."

"Dirham D30,000 kwatankwacin yuro €4,000 ake nema daga hannuna, sune kudin jigilar, ba ni da yadda zan yi na sami wadannan kudin, don haka ba ni da wani zabi sai dai na yi karuwanci", in ji Ada.

Farashi aka yi wa matan gidan na bai daya kuma ita mai lura da su tana rubuta yawan maza da kudin da yarinya ke samu, idan takai iyakar abin da za ta biya shikenan sai ta sallame ta.

Sai da Ada ta yi zaman gidan na kusan shekara biyu da rabi kan ta iya biyan kudin da ake binta.

Ta ce idan za a kwana D300 ake bya idan kuma kwanciyar ta dan lokaci ce D200 ne, kuma ko kwana mutum ya biya, sai kwanta da ita ne sau biyu kacal a daren.

Mafiya wayan matafiyan kan tsintar kansu a wasu sabbin wurare da basu sani ba, ba kuma su yi mafarkin za su taba zuwa ba, wani lokaci ba sa jin yaren kasashen da suke ratsawa ta cikinsu, amma fatan samun rayuwa mai kyau da gujewa wahalhalun da suke ikirarin suna sha a kasashen ne ke kara angiza su.

Lokacin da suke isa Morocoo sukan ji cewa sun ci kashi 80 na wahalar tafiyar ciranin tasu, to amma tsallaka Morocco zuwa Turan a cewarsu, ya fi wuya in aka kwatanta da wahalhalun da suka baro a baya.

Abin da ya sa 'yan ci-rani suka fi son shiga Morocco shi ne, kasar ta hada iyaka da Sifaniya, ta wani gefen tekun za ka iya samun damar shiga Gibrelta daga kasar. Akwai iyakoki masu dama da akan bi amma idan mutum yaje garin Tanja shi ne zai ga cincirundon 'yan ci-ranin.

Hukuma da ke lura da 'yan cirani ta duniya UNHR ta ce yana da wuya a iya sanin adadin 'yan ciranin da ake cin zarafi a lokacin da suke kokarin tsallakawa Turai, saboda dama ba sa fada, kuma tun da tafiyar ba ta kaida ba ce ba su da wanda za su kai wa kara.

Yanzu dai Ada ba ta iya kai wa inda take so ta je ba, kuma a inda ta makale ba ta samun abin da za ta koma gida da shi ta nuna a matsayin ribar tafiyarta.

Sannan gudun jin kunya ka iya sa ta ci gaba da zama a nan, a gefe guda kuma cin zarafin da aka yi ta abu ne da ba zai taba gushewa ba a cikin tunaninta

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN