MAGANIN ULCER CIKIN KWANA 7 DA YARDAR ALLAH.
Idan ka tabbatar da cewa kana fama da cutar gyambon ciki watau ulcer, sai ka jarraba wannan hadin magani da aka zayyana a kasa.
Ko da kuwa wannan cutar ulcer ta haddasa maka matsaloli kamar:
Ciwon baya
Ko ciwon ciki
Ko zafin jiki
Ko zazzabi
Ko kashin majina
Insha Allah wannan fa'ida zata magance maka matsalar ulcer.
ABINDA ZA A NEMA.
1. Cabbage (Kabeji) musamman jan kabeji
2. Garlic (Tafarnuwa)
3. Zuma
YADDA ZA A HADA.
Da farko zaka samu kabeji danye ka yayyanka kanana ka debi kamar cikin hannu sai a samu Tafarnuwa kwayoyin ta guda 2 a samu ruwa kofi 1 sannan a samu blender.
Sai a zuba ruwan kofi daya a ciki a zuba kabejin a ciki da kuma Tafarnuwa sai ayi blending nasu, a juye a kofi sannan a zuba zuma chokali 5 a ciki a sha da safe kafin aci komai.
Insha Allah idan akai na tsawon sati 1 za a samu waraka.
Daga Maijalalaini Islamic medicine
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI