Type Here to Get Search Results !

Tinubu ya yi mummunan kuskure yayin da yake magana a kan Gwamna El-Rufai a Kaduna, yan Najeriya sun mayar da martani

Tinubu ya yi mummunan kuskure yayin da yake magana a kan Gwamna El-Rufai a Kaduna, yan Najeriya sun mayar da martani


Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) (APC), ya yi kura-kurai a lokacin da yake magana kan Gwamna Nasir El-Rufai a taron tattalin arziki da zuba jari na Kaduna karo na bakwai (KADInvest).

Da yake jawabi a wurin taron a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, Tinubu ya ce Gwamnan jihar Kaduna ya mayar da “rubabben yanayi zuwa mummunan hali.”

“Ina rokon Gwamna El-Rufai a fili da kada ya gudu da karin Digiri kamar PhD ko wasu. Akwai masu ilimi,” in ji tsohon Gwamnan Legas.

“Ba za mu bar ku ku gudu ba. Hangen nesanku, kirkire-kirkire da kuma juriya wajen juyar da gurbatattun yanayi zuwa mummunan abu wajibi ne a wannan mawuyacin lokaci kuma shi ya sa muke nan.”

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies