Type Here to Get Search Results !

Kotu ta soke dukkan zabukan fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a wata jihar kudu

Kotu ta soke dukkan zabukan fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a wata jihar kudu


Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas ta soke dukkan zabukan fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Ku tuna cewa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka fusata masu biyayya ga Dan takarar Gwamna na SDP, Sanata Magnus Abe, sun tunkari Kotu suna kalubalantar yadda zaben fidda gwanin ya gudana tare da ikirarin cewa ba a yi zaben fidda gwani na wakilan da aka gudanar a jihar ba.

Wani George Orlu da wasu mutane hudu da suka yi ikirarin cewa sun sayi fom din tsayawa takara sun tunkari kotu inda suka bukaci a soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar sakamakon fitar da su a cikin zaben.

Kotun a hukuncin da ta yanke a jiya, 24 ga watan Oktoba, ta yanke hukuncin cewa ba bisa ka’ida ba an cire mutanen daga zaben fidda gwani.

Justice E.A.  Obile, a cikin hukuncin, ya amince da masu shigar da kara cewa ba daidai ba ne aka cire su a cikin shirin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Don haka ya yanke hukuncin cewa duk wanda aka zaba daga zaben fidda gwani ya soke kuma kada a amince da shi a matsayin ’yan takara.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies