Duba abin da ya faru da wani Bera bayan ya cinye tabar wiwi da NDLEA ta kama (bidiyo)
Wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ya raba wani hoton bidiyo na wani bera da ke shan wiwi.
Mista Femi Babafemi ya ce beran ya samu shiga dakin baje kolin da ake ajiye tabar wiwi a daya daga cikin Hukumar NDLEA.
Bayan ya cinye tabar wiwi sai ya fara shafar bera kamar yadda aka gani a faifan bidiyon da Babafemi ya raba.
Babafemi ya ce dabi’ar bera ya kamata ya zama gargadi ga mutanen da ke shan abubuwan da ke canza hankali.
Kalli bidiyon a kasa.