Zan ba wa matasa kashi 40 cikin 100 na mukamai idan na zama shugaban kasa — Atiku - Isyaku News


Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2023, ya yi alkawarin bai wa matasan ƙasar kashi 40 cikin 100 na muƙamai idan ya hau mulki saboda yadda ya ga ƙwazonsu.

BBC ta ruwaito Atiku Abubakar,  ya bayyana haka ne a baya-bayan nan a wani taro da jam'iyyar ta gudanar a jihar Kaduna.

 A yayin taron, dan takarar da PDP, ya yi bayani a kan irin manufofinsa ga matasa a Najeriya baki Daya.

 Muhammad Kadade Sulaiman, shi ne shugaban matasan PDP a ƙasar, ya shaida wa BBC cewa, a yayin taron da suka yi a Kaduna, Atiku Abubakar, ya ce da ikon Allah idan har ya hau mulki zai farfado da masaku don samar da ayyukan yi ga matasa a Kaduna da ma sauran jihohi.

 Ya ce,” Atiku, na son tafiya tare da matasa domin sune manyan gobe, hakan ne ya sa a duk in da ya je ya ke zama da shugabancinsu don jin irin matsalolin da ke damunsu.”

29 Mayu 2022

Dan takarar shugabancin Najeriyar a PDP, ya ce idan har ka bawa matashi abin yi to ba zai ba da kunya ba in ji shugaban matasan PDPn.

 A yayin kaddamar da yakin neman zabensa, Atiku Abubukar, ya bayyana wasu matsaloli da ya ce kasar na fuskanta kamar batun tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, da shiga matsin rayuwa da al’ummar kasar ke ciki, da kuma batun matsalar tsaro.

 Atikun ya ce, "Rashin haɗin kan da muke fama da shi a yanzu ya zarce na lokacin yaƙin basasa. An wargaza zumuncin da ya haɗe kanmu ta hanyar nuna wariya da rashin amincewa da juna."

 A don haka ya ce, "Shirinmu game da Najeriya shi ne ceto ta ta hanyar adalci da daidaito da haɗin gwiwa tsakanin al'ummominmu mabambanta.

 "Na biyu shi ne kafa gwamnatin dimokraɗiyya wadda za ta saka kwarewa da kuma inganta rayuwar mutane a gaba.

 "Na uku, gina tattalin arziki mai ƙarfi da zai samar da dama ga mutane da ƙasa baki ɗaya.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN