Da dumi-dumi: Yan bindiga sun dira tsakanin garuruwan Marafa da Mahuta sun tafka satar shanu a Masarautar Zuru
Rahotannin sun kara da cewa kawo yanzu ba a sami labarin asarar rayuka ba a harin na ranar Alhamis. Sai dai majiyarmu ta shaida mana cewa jama'a sun yi asara dabbinsu ga yan bindigar wanda suka shiga yankin da sanyin safiyar Alhamis.
Wata majiya da bata son a ambaci sunanta ta shaida mana cewa an gan jami'an soji da yan banga sun shiga yankin domin fuskantar lamarin.
Rubuta ra ayin ka