Akalla mutane 100 ne suka mutu sakamakon haramtacciyar zanga-zanga a kasar Chadi

Masu zanga-zanga a kasar Chadi

Akalla mutane 100 ne aka kashe a kasar Chadi a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da dubban mutane suka bijirewa dokar hana zanga-zanga da suka fito kan titunan babban birnin kasar suna yin tir da gazawar gwamnatin mulkin sojan rikon kwarya na mika mulki ga farar hula.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa zanga-zangar a Ndjamena.

An kuma ji karar harbe-harbe a cewar wani dan jarida na dpa a birnin.

Wasu mutane 300 ne aka ruwaito sun jikkata, kamar yadda Firayim Minista Saleh Kebzabo ya shaida wa taron manema labarai da yammacin ranar Alhamis.

Mahalarta muzaharar, a wasu lokutan, sun kafa shingaye da kona tayoyi.

An kuma bayar da rahoton zanga-zangar daga kananan garuruwa uku. Kebzabo ya yi magana game da wani tashin hankali da ya kamata jami’an tsaro su kakkabe.

Ya sanya dokar hana fita tsakanin tsakar dare zuwa 6 na safe (2300 da 0500 GMT).

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah-wadai da tashin hankalin, ta kuma ce an samu asarar rayuka, ba tare da bayar da wani adadi ba.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi magana game da "amfani da muggan makamai kan masu zanga-zangar" ba tare da bayar da wani karin bayani ba.

Ita ma Faransa ta musanta cewa tana da hannu a abin da ya faru a Chadi.

Ana ta yada ikirarin, musamman a shafukan sada zumunta, cewa Faransa na goyon bayan shugaban na wucin gadi.

Rikicin ya barke ne bayan Mahamat Idriss Deby Itno, shugaban kwamitin rikon kwarya na soji, ya ce za a shafe shekaru biyu kafin farar hula su karbi mulkin kasar. An rantsar da Deby fiye da mako guda da ya wuce.

Kasar Chadi mai arzikin man fetur amma mai fama da talauci ta kasance cikin sauyin siyasa tun a watan Afrilun 2021 da rasuwar tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno, mahaifin shugaban kasar mai ci a yanzu.

‘Yan tawayen da ke neman hambarar da gwamnatinsa ne suka kashe shugaban. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN