DA DUMI-DUMI: Mataimakin Supritandan 'yan sanda ya kashe abokin aikinsa har lahira a garin Argungu jihar Kebbi

DA DUMI-DUMI: Mataimakin Supritandan 'yan sanda ya kashe abokin aikinsa har lahira a Kebbi


Wani mataimakin Supritandan ‘yan sanda wanda har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya kashe abokin aikinsa.

A cewar SaharaReporters, dan sandan ya daba wa abokin aikinsa wuka har lahira a jihar Kebbi.

Marigayin mai suna Shuaibu Sani Malumfashi, mai mukamin ASP, an ce an kashe shi ne biyo bayan rashin fahimtar juna da aka yi tsakaninsa da abokin aikinsa.

Ya kasance jami'in kula da laifuka DCO2 na ofishin 'yan sanda na Argungu da ke Kebbi kafin rasuwarsa.

Majiyoyi sun shaida wa SaharaReporters cewa jami’in da ya daba wa marigayin wuka a halin yanzu yana tsare.

Hakazalika, SaharaReporters ta ruwaito a ranar Litinin cewa, wani Sufeton ‘yan sanda, Ugwor Samuel, da ke tare da dan majalisar dokokin jihar Abia, Hon. Ginger Onwusibe, an harbe shi har lahira.

SaharaReporters ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a Umuahia, babban birnin jihar.

Majiyoyi sun shaida wa SaharaReporters cewa dan sandan da ya mutu, Insifekta Atule Benedict, wanda ke da alaka da dan majalisar daya, Onwusibe ne ya harbe shi.

Wani mai taimaka wa dan majalisar da lamarin ya faru a gaban idonsa ya shaida wa SaharaReporters cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da marigayin ya samu rashin fahimta da abokin aikinsa kan wani tsokaci kan halin Insifeto Atule.

“Atule ya mayar da martani a fusace kuma an samu hatsaniya wanda hakan ya sa sufeto Atule ya dauki bindigarsa ya harbe sufeton da ya rasu,” in ji ma’aikacin.

Mataimakin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce kokarin kwance damarar Atule da wasu ‘yan sandan da ke cikin tawagarsu suka yi ya ci tura, kuma ya yi barazanar kashe ‘yan sanda da yawa idan suka zo kusa da shi.

Daga karshe rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da kisan Insifekta Ugwor Samuel tare da bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin tausayi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN