Yan bindiga sun kai hari Masallaci, sun yi kisa, sun sace dan kasuwa da dansa a jihar Taraba

Yan bindiga sun kai hari Masallaci, sun yi kisa, sun sace dan kasuwa da dansa a jihar Taraba


Wasu masu garkuwa da mutane kimanin su 10 sun kai hari wani masallaci a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a ranar Alhamis
.

Legit.ng ta ruwaito maharan sun kashe mutum daya sun kuma sace wani dan kasuwa da dansa, Daily Trust ta rahoto.

Masu garkuwan sun afka masallacin da ke Jalo Junction ne a unguwar Saminaka na Jalingo da yamma yayin sallar Magariba.

An ce dan dan kasuwan dalibi ne a makarantar sakandare.

Maharan sun tilasta wa mutane da dama yin hijira

Rahotanni sun ce masu garkuwan sun kashe mutane da dama, ciki har da dan sanda tare da sace fiye da mutane 30 a cikin yan watanni.

Masu garkuwa da ke kai hare-hare a tsaunikan har zuwa rafin Lamurde a karamar hukumar Ardo_Kola sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, amma ba a iya samunsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

'Yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.

A lokacin da suka zagaye masallacin, sun bukaci duk wadanda ke wajen masallacin da su shiga ciki cewa sun zo ne domin tattauna kan yadda zasu sako wasu mutanen dake hannunsu.

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 a Masallaci a Kaduna, Sun Kuma Sace Mata Da Dabobbi

A wani rahoton, kun ji cewa an sace wasu masallata a yayin da yan bindiga suka kai hari a masallaci a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun kai harin ne lokacin da mutanen ke sallar Ishai a ranar Alhamis.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN