An kama wasu matasa biyu da ake zargi da kwarewa wajen samar da sanarwar alert na karya don zambatar masu POS - ISYAKU.COM

An kama wasu matasa biyu da ake zargi da kwarewa wajen samar da sanarwar alert na karya don zambatar masu POS


Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wasu mutane biyu da ake zargi, Ofemu Obus ‘m’ mai shekaru 23 da kuma Henry Ekpu mai shekaru 28, wadanda ake zargin sun kware wajen damfarar ma’aikatan POS da ba su ji ba, ta hanyar samar da sanarwar alert na bogi da suke amfani da su wajen yaudarar wadanda abin ya shafa don su zambace su kudinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, wanda ya tabbatar da kama su, ya ce wadanda ake zargin suna tsare kuma suna fuskantar bincike.

A wani labarin kuma, ‘yan sandan jihar sun kama wasu masu laifi biyu da ke amfani da babur uku wajen kai hari ga ‘yan jihar da ba su ji ba, sannan su kwace wayoyinsu na iPhone.

Edafe ya ce an kama mutanen ne a lokacin da tawagar sintiri na Dragon 29 da 26 suka gudanar da bincike a kan hanyar Warri-Sapele a karamar hukumar Okwuvo Okpe.

Ya bayyana cewa babur Daylong tare da Reg.  No. Delta UGH 353 VQ dauke da maza biyu an kama su.  ‘Yan sandan sun gudanar da bincike a kansu inda aka gano, iphone daya (1) wayar Infinix, daya (1) wayar Nokia torch.

A yayin da ake gudanar da bincike, masu wayoyin sun fara kira, kuma sun yi zargin cewa suna Sapele da Oghara.  Daga baya an bayyana sunayen wadanda ake zargin John Francis ‘m’ mai shekaru 26 mazauni Uru-Ughelli Street Agbarho da Godsent Orogun ‘m’ mai shekaru 25 mazauni gida mai lamba 18 Ovwiagba.  Wadanda ake zargin suna tsare yayin da ake ci gaba da bincike.'' inji shi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN