An kama Sojoji da laifin satar alburusai tare da sayar wa 'yan Boko Haram da 'yan bindiga (bidiyo)
Sojojin Najeriya mai hidima na sirri; An kama Emmanuel Iorliam na bataliya ta 156 Task Force Battalion da ke Mainok a jihar Borno da laifin gudu da bindiga.
Iorliam wanda ya fito daga jihar Binuwai, ana zarginsa da satar makamai da alburusai daga sansaninsa wanda yake sayarwa ga ‘yan bindiga, ‘yan Boko Haram, da masu garkuwa da mutane. Ya gamu da Waterloo din sa ne, watau asirinsa ya tonu ne a lokacin da yake fitar da tarin alburusai daga jihar Borno domin mikawa kwastomominsa.
Abokan aikinsa ne suka tare shi a wani shingen binciken ababen hawa, inda suka yi bincike aka gano yana da harsashin da aka sace.
Wani faifan bidiyo da aka watsa ta yanar gizo ya nuna lokacin da abokan aikinsa suka kama shi da kayan da aka sace.
Kalli bidiyon a kasa