Iyayen jarirai 4 da aka haifa a asibitin garin Koko a jihar Kebbi na neman taimakon gaggawa daga jama'a, duba dalili


Malam Umaru Faruku da matarshi Nafisa Umaru da ta haifi yara jarirai hudu a babban asibitin garin Koko a jihar Kebbi na matukar neman taimakon bayin Allah.

Majiyarmu ta shaida mana cewa sakamakon wannan arziki da Allah ya ba iyalin, suna neman taimakon gaggawa domin samun sukunin hidimtawa ga jariran.

Sakamakon haka suke mika kokon baransu ga jama'a domin neman taimako don Allah.

Dubu hoto a kasa dauke da lambar asusun banki da za a iya mika taimakon da kuma lambar waya domin tumtubarsu kai tsaye. 

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE